Header Ads

Yadda Za a Kawo Karshen 'Yan Ta'addan Dake Zamfara Inji Gwamna Abdul'aziz Yari

Gwamnan jihar Zamfara Abdulaziz Yari ya ce sai gwamnatocin jihohin da ke makwabtaka da jiharsa sun hada gwiwa, kafin a samu nasarar fatattakar 'yan bindiga da ke addabar al'ummar yankin.

Ya bayyana hakan ne lokacin wata hira da ya yi da BBC a Abuja ranar Laraba.
Jihar Zamfara na fara da matsalar hare-haren 'yan bindiga da satar mutane ana karbar kudin fansa.
Gwamnan ya ce akwai bukatar a bai wa sojoji manyan bindigogi wajen yaki da mahara da ke yankin.
Har ila yau ya ce karfin maharan "bai yi kusa da na jami'an tsaron Najeriya ba."
"Sojojin Najeriya suna da horo, suna da kayan aiki, suna da izini. Wadannan kuma ('yan bindigan) suna aiki ne na ta'addanci, ta ina ne karfinsu zai zama daya?"
Ya ce maharan suna amfani ne da bindigogi "na al'ada" wato kanannan bindigogi.
"Yayin da jami'an tsaro suke amfani da manyan bindigogi saboda da haka wadannan manyan bindigogin ne muke so jami'an tsaro su fito su yi amfani da su," in ji shi.
A karshe ya ce ya kamata sojoji su nuna wa wadannan maharan ba sani, ba sabo wajen yaki da su.

No comments

Powered by Blogger.