Header Ads

Yadda Ozil Ya Turama Wani Yaro Takalmin Kwallo Da Riga Ta Arsenal

Dan wasan Mesut Ozil ya aika wa wani yaro takalmin kwallo da rigunan Arsenal da ke dauke da sunansa harda singing dinshi me nuna shine ya aikama yaron dakanshi


Lawrence Masira mai shekara 12 dan kasar Kenya ne kuma babban magoyi bayan kungiyar Arsenal.
Yaron dan kabilar Maasai ya rubuta sunan Mesut Ozil ne a bayan wata rigar kwallo kamar ta Arsenal da mahaifiyarsa ta saya ma shi.
Hoton yaron da aka dauka aka wallafa a intanet ne ya ja hankali har Ozil ya gani.
Yaron ya ce Ozil ne gwaninsa a Arsenal saboda yadda yake taka leda da kuma yadda yake taimakawa Arsenal cin kwallaye.
An ta yada hoton yaron sanye sanye da rigar kwallo yana kiwon shanu a Twitter wanda wani dan jarida ya dauka.
Dan jaridar ne ya fara wallafa hoton kuma ya alakanta hoton zuwa ga Ozil don ya taimakawa Yaron.
Nan take Ozil ya aikawa dan jaridar da sako cewa ya ji dadi kuma yana son taimakawa Yaron.
Ozil ya aiko wa yaron da takalmin kwallo da riguna Arsenal dauke da sunansa ta hanyar dan jaridar mai suna Eric.
Yaron ya ce ya ji dadi kuma yana fatan wata rana zai yi ido biyu da Ozil.

No comments

Powered by Blogger.