Header Ads

Wata Sabuwa Kan Kisan Musulmai 49 Facebook Ya Fuskanci Kalubale

Kamfanin sada zumunta na Facebook ya bayyana cewa mutumin da ya kai hari a masallatan nan biyu da ke birnin Christchurch a New Zealand ya yi amfani da Facebook domin yin bidiyo kai tsaye kan yadda ya kai hari a masallatan.
Bidiyon da ya watsa kai tsaye a lokacin da ya kai harin, mutane kasa da 200 ne suka kalla bidiyon a lokacin da yake watsa shi.
Bayan dan bindigan ya kai harin, shafin Facebook ya fuskanci matsin lamba daga bangarori daban-daban a kan cewa su goge bidiyon sakamakon irin tashin hankalin da ke cikin biyidon.
Ko kafin Facebook ya goge shi, an kalli bidiyon kusan sau 4,000.
Kafofin sada zumunta sun yi iya bakin kokarinsu domin hana yaduwar wannan mummunan bidiyon amma duk da haka yana yawo a kafofin.
Facebook appsHakkin mallakar hotoGETTY IMAGES
Duk da cewa ainahin bidiyon da wanda ya kai harin ya nada a shafin Facebook an goge shi, jama'a da dama tuni suka yi ta yada wannan bidiyon a Twitter da kuma YouTube.
Kamfanin Facebook ya bayyana cewa ya goge sama da irin wannan bidiyon miliyan daya da dubu dari biyar a ranar da lamarin ya faru.
Kamfanin ya kuma bayyana cewa an yi kokarin toshe kusan miliyan daya da dubu dari biyu a lokacin da ake kokarin tura su.

Sanin yakamata

Ana ci gaba da sukar halin ko in kula da kafafen sada zumunta ke nunawa wajen matakin da suke dauka kan munanan abubuwan da ake wallafawa.
Shugaban Australia Scott Morrsion ya bayyana rashin jin dadinsa ta yadda aka saki intanet sakaka ana amfani da ita "ana ta'addanci."
A wata takarda daya rubuta wa Firai Ministan kasar Japan Shinzo Abe wanda shi ne shugaban kungiyar kasashe 20 masu karfin tattalin arziki na G20, ya bukaci a tattauna kan wannan batun a zaman da za su kara yi nan gaba.
Ya bayyana cewa ''ba daidai ba ne a ce ba doka ko baza a sa ido a shafin intanet ba.''

Me masu talla a shafukan intanet ke cewa?

A daidai lokacin da ake cikin jimamin kisar gillar da aka yi a masallatai a New Zealand, bankin ajiya na Westpac ya ce ya dakatar da duk wasu tallace-tallace da yake bayar wa a kafafen sada zumunta har da Facebook, sai har sai baba ta gani.
Kamfanin ya bayyana wata sanarwa a shafin Twitter inda ya ce "za mu rinka tattaunawa da kamfanonin sada zumunta kan wallafa abubuwa masu cutarwa.''
A ranar Litinin mai magana yawun kamfanin Lotto a New Zealand ya ce sun cire tallace-tallacen su daga kafafen sada zumunta a wannan lokaci sakamakon yanayin da aka shiga bayan da wannan lamarin ya faru kasar.

No comments

Powered by Blogger.