Header Ads

UEFA Taci Ronaldo Tara Kan Murnar Cin Kwallo

Hukumar kwallon turai Uefa ta ci tarar dan wasan gaban Juventus Cristiano Ronaldo saboda murnar kwallayen da ya ci Atletico Madrid a gasar zakarun turai.

Ronaldo mai shekaru 34, ya kwaikwayi yadda kocin Atletico Diego Simeone, ya yi tasa murnar a fafatawar farko da Atletico ta doke Juventus 2-0 a Spain.
Dan wasan ya juwa cikin 'yan kallo da kafafuwansa bude yana ihu domin murnar kwallo ta uku da ya jefa a ragar Atletico a karawa ta biyu a Italiya.
Kwallaye uku rigis da Ronaldo ya ci ne ya taimakawa Juventus nasarar tsallakawa zagayen wasan daf da na kusa da na karshe.
A ranar 21 ga Maris ne hukumar Uefa za ta zartar da hukunci kan laifin na Ronaldo.
Tun da farko, Kocin Atletico an ci tararsa kudi har fan dubu 17, wanda ya yi daidai da Naira miliyan 8.
Juventus da ta fitar da Atletico an hada ta wasa ne da Ajax wacce ta yi waje da Real Madrid da ta lashe kofin sau uku a jere.

3 comments:

  1. I recently came across your blog and have been reading along. I thought I would leave my first comment. I don't know what to say except that I have enjoyed reading. Nice blog. I will keep visiting this blog very often. https://www.ngoac.net/tin-tuc.html

    ReplyDelete

Powered by Blogger.