Header Ads

An Tafka Kuskure Wajen Daga Zaben Bauchi

Hukumar zaben Najeriya mai zaman kanta INEC ta ce za ta ci gaba da tattara sakamakon zabe na mazabu da rumfunan zabe domin hada sakamakon karamar Tafawa Balewa a zaben gwamna da na 'yan majalisar dokoki na jiha.
Hukumar ta nada sabon jami'in zabe da zai ci gaba da tattara sakamakon, wanda kuma zai maye gurbin tsohuwar jami'ar tattara sakamakon wacce ta janye daga aikin saboda barazana da tace tana fuskanta.
A makon jiya ne hukmar zaben ta Najeriya INEC ta bayyana cewa zaben jihar Bauchi bai kammala ba, kuma za a sake zabe a karamar hukumar Tafawa Balewa, saboda rashin samun sakamakon zaben kamar yadda dokokin zabe suka tanada, bayan tashin hankali yayin tattara sakamakon.

INEC ta ce za ta yi amfani da kwafin takardun da aka rubuta sakamakon zaben a kansu a mazabu, wadanda daga nan za a samu sakamakon karamar hukumar.
Sannan hukumar ta ce gano cewa akwai kuskure wajen lissafin kuri'un da aka soke a rumfuna hudu a karamar hukumar Ningi inda aka ce sun kai 25,330, maimakon 2,533 wadanda INEC din ta ce su ne alkaluma na gaskiya.
Hukumar ta ce a yanzu za a sake lissafi da alkaluma na gaskiya na kuri'un da aka soke a karamar hukumar Ningi da suke 2,533.
Wannan layi ne
Abinda INEC ta gano
Hukumar ta zabe INEC ta kafa wani kwamiti ne da zai bincika abubuwan da suka faru a Bauchi bayan da jami'in tattara sakamakon gwamnan jihar ya ki karbar sakamakon karamar hukumar Tabawa Balewa.
Baturen zaben ya ki karbar sakamkon ne saboda ba a rubuta shi a kan takardar da INEC ta amince a rubuta sakamakon karamar hukuma a kai ba.
Bisa haka ne da farko aka ce za a sake zabe a karamar hukumar ta Tafawa Balewa, kafin yanzu hukumar ta sauya matsayinta.
An yi zaben gwamna da na majalisar wakilai ranar 9 ga watan Maris a Tafawa Balewa, kuma an bayyana abinda kowane dan takara ya samu a matakin mazabu 11 dake karamar hukumar.
Bayan binciken hukumar ta INEC ta gabo cewa
  • Ana tsaka da aikin tattara sakamakon ne wasu mutane dauke da makamai suka afkawa cibiyar tattara sakamakon ta karamar hukuma, sannan suka lalata takardar shigar da sakamako ta karamar hukuma (EC8C), da kuma sakamakon wasu mazabu. An lalata sakamakon mazabu bakwai ne daga cikin 11 da ke karamar hukumar.
  • Dokokin zabe sun tanadi cewa duk inda rikici ya hana a tattara sakamako a irin wannan yanayi, za a yi amfani ne da kwafin sakamakon da aka tattara a matakin mazabu kan takardar maye gurbin sakamako.
  • Jami'ar zaben karamar hukumar ta rubuta sakamakon zaben karamar hukumar a kan takardar rubuta sakamako ta mazaba, maimakon na karamar hukuma, saboda yadda wakilan jam'iyyu suka ringa matsa mata lamba.
  • Yayin da aka gabatar da sakamakon ga baturen zaben gwamna na jihar Bauchi, ya yi watsi da shi saboda ba a rubta shi a kan takaradar da ta kamata ba.
  • Kwamitin binciken ya gano cewa akwai sakamakon mazabu da rumfunan zabe a hannun mutane.
  • Binciken ya kuma gano cewa na yi aringizon kuri'un da aka ce an soke a mazabu hudu dake karamar hukumar Ningi, inda aka rubuuta kuri'u 25,330 maimakon 2,533 da su ne ainihin abinda aka soke.
A ranar Talata ne INEC za ta ci gaba da tattara sakamakon zaben na Tafawa Balewa inda daga nan kuma ake sa ran bayyan sakamakon zaben gwamnan na Bauchi.

No comments

Powered by Blogger.