Header Ads

Duniya Na Kallo Kuna Zubarwa Da Nijeriya Mutunci, Nasihar Buhari Ga `Yan Majalisar TarayyaDuniya Na Kallo Kuna Zubarwa Da Nijeriya Mutunci, Nasihar Buhari Ga `Yan Majalisar Tarayya
A cikin wani yanayin na ban-tausayi, Shugaba Muhammadu Buhari ya shawarci ‘yan Majalisar Tarayya da su daina tozarta Nijeriya a lokacin da duk duniya ke kallon abin da ke gudana a zauren majalisar.
Hakan ya biyo bayan cin fuskar da Buhari ya fuskanta da kuma tozarta shi da wasu mambobi suka yi, a lokacin da ya ke gabatar da kasafin kudi na 2019.
An rika yi masa ihu da sowa da furta ba ma yi, ba mayi. Wasu ma sun rika wuce gona da iri, su na cewa karya ce.
A cikin tattausar zuciya, shugaba Buhaeri ya roki mambobin da su daina abin da suke yi, domin duniya gaba daya na kallon abin da ke faruwa.
Buhari ya shaida musu cewa wannan ne kasafin kudi na karshe da zai gabatar wa majalisar a wannan zango na sa.
Ya dai sake tsayawa takarar shugabancin kasa a karo na biyu, wanda idan bai yi nasara ba, wannan ne zai kasance kasafi na karshe da ya gabatar a zauren majalisar.
A baya ya gabatar da na 2016, 2017, 2018 da kuma na yau, 2019.
MUN FUSKANCI KALUBALE A SHEKARU UKU BAYA
Buhari ya tabbatar musu da cewa a sheakaru uku da suka gabata, Najeriya ta fuskanci babban kalubale, amma kuma tattalin arzikin ya fita daga cikin halin kaka-ni-ka-yi da kasar nan ta tsinci kan ta.
Ya yarda da cewa wasu ayyukan ci gaban da aka kasa gudanarwa ya faru ne dalilin matsalar tsaro a cikin kasar nan.
ZA MU KAWAR DA MATSALOKIN BOKO HARAM DA RIKICIN MAKIYAYA DA FULANI
Duk da dai ya na magana ana karyata shi, Buhari bai daina furta inda kasar nan ta sa a gaba ba, har ya ci gaba da bayanain cewa an dauko hanyar magance matsalar makiyaya da kuma manoma da rikicin Boko Haram.
HALIN DA ASUSUN NAJERIYA KE CIKI
Shugaba Muhammadu Buahri ya shaida cewa a hanlin yanzu, lalitar Najeriya ta kasashen ketare adadin ta ya kai dala bilyan 42.92 ya zuwa cikin wannan wata na Disamba, 2018. BY KADUNAWEB.COM

No comments

Powered by Blogger.