Header Ads

Assalamu alaikum kuna tare da da babban shafiAssalamu alaikum kuna tare da da babban shafi
mai suna
shafin da ya kware wajen kawo muku darasi akan abinda suka shafi fasahar zamani
darasin da zamu gabatar yau zamu yi ne akan masu samun matsalolin sa Security a wayar su daga bisani suka manta
To kamar yadda wasunku sunsan ana iya cire security na waya batare da kaje computer ka biya kudi an cirema ba to saide
kuma mutane dayawa basusan cewa akwai yadda xa kuyi ku cire security kwata kwata sabo da shi wanda mutane suka sani kawai ana iya cire shine a time din da mutum xaiyi amfani da waya amma idan ya kasheta inya kunnan to dole sai ya sake pitarwa, tam ni yanxu abin da xan yi bayani akansa shine
ZANYI BAYANI AKAN YADDA ZAKA FITAR DA NA KO WACE IRIN WAYA
TO AMMA BARI MU FARA DA ANDROID PHONE
YADDA ZAKA BUDE KO RESET DIN SECURITY CODE DIN
WAYAR ANDIRIOD BAYAN KAMANTA
A Yau yawancin Mutane Suna Amfani da waya Kirar Andiriod Dan Amfanin kansu. Hakan ne Nema yasa Wasu
Lokuta Wasu ke Sa
Security Code A wayar Tasu, Domin su Tsare wayar Tasu Daga Muta Ne Saboda Mantuwa Ko kuma mu iya Cewa Harkoki Sunma Wasummu Yawa,
Saikaga Mutum ya manta ko Meya Seta A Matsayin Pasword din nasa, Daga nan kuma Sai a shiga Ruda ni, Sai ankaita Anyi UNLOCKING dinta, Inma Anyi Rashin Sa'a Saikaji Ance sai Anmata Flashing..... Idan kaima kasamu kanka cikin wanda yasa Security Code Na
Wayarsa Kirar Andriod, Kuma ya manta
GA MATAKAN DA ZAKA BI KAMAR HAKA
Da Farko-: Ana bukatar Ka kashe wayar Taka
Mataki Na Biyu-: Saika danna key din Volume Na Sama, Yayi tsahon 30 Seconds
Amma wata batai da Volume din sama sai dai na kasa
Mataki Na Uku 3 -: Saika danna Key din Kunna wayar wato Power button
A tare Har sai wayar Takawo, Tana kawo wa saika Saki key din da ka daddanne,
Wato Volume da Switch Key
Mataki Na Hudu-: Da ganan ne zakaga ta
Nuna maka wani Error
wata kuma xata fara nuna maka wasu zabuka ne
idan ta nuna maka zabuqa ne sai ka shiga
== >>Recover mode
idan kuma Error ta fara nuna maka sai ka danna
Power button sau 1
zaka ga ta jero maka wasu
Rubutu MENU
sai
kayi amfani da
Volume key wajen control kasa ko sama
domin touch bazai aiki ba a wajen
shi kuma Power button shine a matsayin Click din ka
sai ka shiga
== >>Reset Data Factory
bayan ya bude sai kayi kasa ka shiga
Saika danna Zabi Na Uku Wato
== >> " Delete All User Data "
Daka Danna
anan take zata fara seaching
Kasani ba,a katseta yayin da take gudanar da wannan aikin
koda kuwa kaga ta dadene bata gama wannan seaching dinva
idan kuma har ka kuskura kai gajin haquri ka cire battery ko kai wani abu da yasa ta yanke wannan aikin da take yi
to tabbas files din wayar zasu sami matsala wadda zata kaiga dole kai mata plashing
Ci gaban darasi
bayan ta gama wannan seaching din
Shikenan Kaci Nasaran Reset Din Security Code din wayar Andriod Dinka.
daga nan sai kayi
Rebot dinta
SAURA KUMA NA WAYAR NOKIA S40
idan kaji ance maka Nokia s40 ana nufin wayoyi kamar irin su
Nokia asha c1, c2, 210, 2700
da sauran su
To da parko idan wayar ku kirar Nokia s40 ta shiga security
kuma kuka manta yadda kukasa pin din to
GA YADDA ZAKU YI
kawai ku kashe wayar sannan ku kunnata
sai kudanna
== >> 112
sai kuyi ready da hannun ka daya wajen danna calling daya kuma wajen danna Back
daga nan sai ka danna Calling
kai kuma sai kayi sauri ka caccaka back ma,ana ka daddana back na wayar da sauri
karka bari kiran ya tapi
anan take security wayar zai fita
to amma kusani shi wannan hanyar da bawai ya fita vane har abada xai dawo duk wayayin da ka kashe wayar ko kai kira
sai dai kuma ka kara danna 112 kayi amfani da ma takan da muka bayar ka kara cire ta
Wannan abu na gwadashi a wayoyi da dama kuma yayi na gwada ne da Asha 200 da kuma nokia c2-00 da nokia 2700 nokia 210,
wannan shine na cire nokia
SAURA NA CHINA PHONE
Shi kuma na china phone yafi ko wanne sauki
Ga matakan kamar haka
ka kashe wayar sannan idan ta nuna maka kashiga da Security sai ka danna 112
ka calling da zarar kiran ya tafi sai kai sauri ka danna
*#12345#
zata tambaye ka
Do you want clear all data?
sai ka danna
YES
insha Allah itama zata fita
amma wannan tricks din yana aiki ne a CHINA PHONE na TECNO da ITEL
Sannan zaka iya amfani da wadan nan codes din wajen dawo da security waya sabo wanda aka rigada aka sanja
Mun koyar da wannan darasi ne domin taimakawa jama,a bawai dan nunawa barayi hanyar cuta va
pls idan ka karu da wannan darasin kai Share zuwa fb,whatsapp domin jama,a su karu

No comments

Powered by Blogger.