Header Ads

Ya Kashe Jaririnsa sa Sabida Bashi

Ya Kashe Jaririnsa sa Sabida Bashi Da Kudi Saya Masa Ragon Suna

Rashin kudin siyan rago ya haddasa wannan magidanci ya kashe dan cikin shi
Habibu Bala ya amsa laifin aika-aikar da ya tafka yayin da aka bayyanar dashi gaban manema labarai a hedkwatar rundunar yan sanda dake nan garin Bauchi.

Hukumar yan sanda na jihar Bauchi sun cafke wani magidan mai suna Habibu Bala mai shekaru 25 bisa ga kashe dan cikin shi da gangan.

Matashi wanda ya fito daga karamar hukumar Ningi nan jihar Bauchi ya aiwatar wannan mummunar lahani ga danshi bisa ga bassusuka da ci kan dawainiyar hidimar bikin suna. A cewar shi ya yanke shawarar kashe jaririn nashi ne bayan bai samu kudin siya ragon suna.
Matashi wanda ya fito daga karamar hukumar Ningi nan jihar Bauchi ya aiwatar wannan mummunar lahani ga danshi bisa ga bassusuka da ci kan dawainiyar hidimar bikin suna. A cewar shi ya yanke shawarar kashe jaririn nashi ne bayan bai samu kudin siya ragon suna.
Habibu Bala ya amsa laifin aika-aikar da ya tafka yayin da aka bayyanar dashi gaban manema labarai a hedkwatar rundunar yan sanda dake nan garin Bauchi.
Ya ce, yana da sana’ar da yake yi na leburanci, inda ya ce shi gaskiya ba shi da wadanda ma za su taimaka masa da kudin da zai yi sunan dansa “gaskiya ni ban ga wadanda za su taimaka min ba, amma ina da ‘yan’uwa a kuma daidai lokacin ni ban ga wanda zai taimake ni da kayan suna ba. da fiya-fiya na kashe yarona..
Ya kuma kara da cewa, “Na yi matukar damuwa da na kashe dana na kaina, dan kwanaki biyar a duniya, na tausaya masa kuma na tausaya wa kaina..
Matashin dai ya bayyana cewar tabbas ya yi matukar kaduwa da aikata wannan munnunar aika-aikar da ya yi wa kansa, yana mai bayanin cewar ya shiga cikin damuwa fiye da tunanin dukkanin wani mutum don haka ya bayyana cewar bai san yadda zai yi ba.
Da yake karin bayani ga manema labaru, Kakakin Rundunar ‘yan sandan jihar Bauci, DSP Kamal Datti Abubakar, ya bayyana cewa, dan’uwan mahaifin jaririn ne ya kawo masu rahoton aukuwar lamarin, inda su kuma su ka kamo mahaifin jaririn bisa laifin kisan kai,
DSP ya kara da cewa, “An hanzarta da jaririn zuwa asibitin Ningi amma rai ya yi halinsa a wajen likita, inda likitan ya tabbatar da mutuwar jaririn a sakamakon wannan fiya-fiyar da Ubansa ya shayar da shi”.
DSP Datti ya ce, wanda suke zargi kuma mahaifin jaririn ya amince da laifinsa da bakinsa don haka suna nan suna shirye-shiryen gurfanar da shi a gaban kuliya bisa laifin kisan kai.

No comments

Powered by Blogger.