Header Ads

AN GANO WATA MATSALA KAN CERTIFICATE DIN BUHARI S

AN GANO WATA MATSALA KAN CERTIFICATE DIN BUHARI S

Darussa biyu da sukayi layar zana a sabon shaidar Jarabawar gama sakandare na shugaba Muhammadu Buhari
- Babu sakamakon lissafi da sarrafa itace
- A sakamakon da WAEC ta bada a 2015 kuwa, darussa 8 ne
An sake gano wasu matsalolin daga satifiket din makarantar Buhari

Darussa biyu sunyi layar zana a sabuwar shaidar WAEC ta Buhari. Sakamakon 2015 na kunshe da darussan : English Language, Hausa Language, Literature-in-English, History, Geography, Mathematics, Health Science and Wood Work.

Amma a Mathematics da wood work shugaban ya fadi ; shin ko hakan ne yasa aka cire sakamakon su a shaidar da aka bashi ranar juma'a, 2 ga watan Nuwamba,2018?

Amma a Mathematics da wood work shugaban ya fadi ; shin ko hakan ne yasa aka cire sakamakon su a shaidar da aka bashi ranar juma'a, 2 ga watan Nuwamba,2018?

Majiyar mu ta gano cewa shaidar dai bata dauke da darussan biyu. Amma a shaidar da WAEC ta bada domin zaben 2015, mai dauke da suna Mohamed Buhari, tare da hatimi mai kwanan wata 21 ga watan daya, 2015, darussa takwas ne.

Sanarwa: Shafin WWW.KADUNAWEB.COM Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa..

No comments

Powered by Blogger.